Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar dokokin jihr Nasarawa Muhammed Baba Ibaku yace suna nan akan bakansu na tsige gwamnan jihar amma doka bata basu damar gudanar da harkokin majalisar a wani wuri ba.
Baba Ibaku yace hedkwatar jihar Nasarawa na Lafiya ne sabili da haka babu inda zasu je su zauna sai garin Lafiyan. Yace duk inda suka zauna dole a samu sandar majalisa. Idan babu ita to komi suka yi banza ne. Yace duk raderadin cewa zasu zauna a Abuja karya ne.
Dangane da cewa 'yan majalisa da bangaren gwamnati suna Abuja Baba Ibaku yace su basu a Abuja. Suna hutu ne. Kowa yana zama inda yake. Batun ba gwamnan takardar zargin da su keyi masa yace ba gwamnan takarda ya gagara sabili da haka sun buga zargin a jarida. Doka tace a bashi hannu da hannu ko a buga a jarida. Yace doka tace a ba gwamnan kwana goma sha hudu. Idan wa'adin ya cika zasu dawo.
Batun zanga-zanga da mutane keyi Baba Ibaku yace wanda ya sa zanga-zangar shi zai ce su bari. Majalisa bata shirya wani zanga zanga ba. Yace shin wanda ya kama barawo ne mai laifi ko barawon.
Abdulhamid Yakubu Kwara mai ba gwamnan shawara akan harkokin jama'a yace suna Abuja ne domin gwamnan yana da bita a ofishin jakadancin Amurka. Ya gama bitar kuma zai koma Lafiya. Yace kawo lokacin da yake magana 'yan majalisar basu basu takarda ba. Yace kundun tsarin mulkin Najeriya bai ce 'yan majalisar su buga zarginsu a cikin jarida ba.
Sakataren jam'iyyar APC a jihar Nasarawa Aliyu Bello yace "da walakin goro a miya" domin abun dake faruwa ya nuna boka yana Abuja domin an ce kowa yana Abuja. Yunkurin tsire gwamnan ba zai kawowa jihar alheri ba. Ban da 'yan majalisa hudu dake Lafiya duk sauran suna Abuja kuma a Lafiya ake zabe ba a Abuja ba.
Shugaban matasan PDP na jihar Muhammed Barde Agwai yace zargin da a ke yiwa jam'iyyarsu ba'a yi masu adalci ba. Duk wanda yace PDP ce take haddasa abun dake faruwa bai yi mata adalci ba.
Ga karin bayani daga Zainab Bababji.