WASHINGTON, DC —
Baban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon ya baiyana damuwa akan rahotanin dake cewa, wata kotun kasar Masar ta yankewa magoya bayan haramtattaciyar kungiyar Muslim Brotherhood hukuncin kisa.
A wata sanarwar daya gabatar jiya Litinin, Mr. Ban yace a filli ne cewa babu alamar anyi adalci a hukuncin da aka yanke.
Itama Amirka tace ta damu da wannan hukunci. An dangata shari'ar da aka yi musu da mumunar tarzomar data barke a Minya da wasu wurare a Masar, bayan da jami'an tsaro da karfin tsiya suka tarwatsa zanga zangar da magoya bayan kungiyar Muslim Brotherhood suka yi a watan Augustan bara.
Kungiyar Muslim Brotherhood ta gabatar da wannan sanarwa dake cewa zata ci gaba da amfani da hanyoyin lumana wajen kawo karshen mulkin soja a kasar.