Kungiyar dake kula da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, tace hanyoyin da za'a bi domin magance matsalolin da yan gudun hijira ke fuskanta shine a maida su garuruwan su, da aka tabbata an samu zaman lafiya.
Mr Edward Kallon mai kula da harkokin yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, shine ya baiyana haka a lokacinda ya ke ganawa da yan gudun hijira a sansanin yan gudun hijira na Bakassi dake Maiduguri, jihar Borno arewa maso gabashin Nigeria.
Mr Kallon ya gana da yan gudun hijira ne a wannan rana da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe domin nazari da kuma jawo hankalin duniya ga matsalolin yan gudun hijira a duk fadin duniya.
Yace a arewa maso gabashin Nigeria farar hula, da mata da maza da yara kanana sune suka fi fuskantar matsanancin keta hakkin bil Adama harma da matsalar fyade.
Mr. Kallon yace tun lokacinda aka fara kai hare hare a 2009, an kashe fiye da mutane dubu ashirin anyi garkuwa da dubban mata da yara. Sa'anan kuma ana ci gaba da amfani da yara wajen kai hare haren kunar bakin wake.
Facebook Forum