Majalisar Dattawan Najeriya ta yi watsi da yunkurin yi wa jadawalin zaben shekara mai zuwa garambawul.
Hakan ya faru ne saboda yunkurin bai samu isasshen goyon baya ba da gyaran ya fuskanta a majalisun wakilai da na dattawa lokacin da aka gabatar da shi a zamansu.
Mambobin sauran jam'iyyun sun yi tir da yunkurin musamman ma a majalisar dattawa jim kadan bayan da shugaban kwamitin zabe na majalisar Suleiman Nazir ya yi kokarin farfado da maganar.
Duk da umurnin da mataimakin shugaban majalisar dattawan ya bai wa kwamitin cewa yana iya sake waiwayar maganar, Sanata Kabiru Gaya nan take ya hango abun da ya kira sakin layi.
Ya ce babu amfanin yi wa jadawalin garambawul a daidai lokacin da suke kokarin rage kashe kudi akan zabuka.
Kamata ya yi a samu yadda za'a tallafawa talakawa ba a kasa zabe gida uku ba. Yadda hukumar zabe ta shirya a yi shi ya fi alheri, injishi.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.
Facebook Forum