Sanata Aliyu Sabi Abdullahi mai magana da yawun Majalisar Dattawan Najeriya yace wasikar gayyatar shugaban hukumar kwastan tun 9 ga watan nan na Maris aka aika masa amma washegari sai ya sa wani kasa dashi kasa da mataimakinsa ya ba Majalisa amsa cewa shi ba zai samu zuwa ba saidai a sake masa rana.
Bisa ga cewar Sanata Abdullahi, dalilin neman da ya nemi a bashi wata ranar daban shi ne taron da shi shugaban kwastan Hamid Ali yace ya shirya zai yi wata ganawa da ma'aikatansa a wannan ranar, wato gobe kenan. Sanata Abudullahi yace jin hakan ya sa Majalisa ta fusata saboda tana ganin Hamid Ali ya rainata ne.
Irin wannan halin da shugaban kwastan ya nuna, Sanata Abdullahi na ganin shi yake kawo matsala tsakaninta da bangaren masu zartaswa.
Yace, Taron da shugaban kwastan din zai yi gobe shi ya shiryashi kuma yana iya dageshi har zuwa wani lokaci ko wata rana saboda haka Majalisa bata amince masa ba, dole ne ya bayyana gabanta gobe. Ita Majalisar Dattawa tana gaba da ministoci balantana wadanda suke aiki a karkashin ministocin, inji Sanata Abdullahi.
Dangane da dagewar Majalisar cewa dole ya sa kayan sarki kafin ya bayyana a gabansu, mai magana da yawun Majalisar yace aikin kwastan ya tanadi sa kayan sarki. Idan kuma Hamid Ali ba zai sa kayan sarki ba sai ya nemi wani aikin.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.
Facebook Forum