Majalisar Dattawan Najeriya ta fitar da wani sabon matsayi kan tantance jami'an da gwamnatin tarayya ke so ta nada a mukamai daban-daban.
Majalisar wacce ta nuna rashin jin dadinta kan kin cire Ibrahim Magu duk da cewa ta taki tabbatar mai da mukaminsa, a baya-bayan nan ta ki tantance Mr Lanre Gbajabiamila da bangaren zartaswar ya mika mata.
Daga cikin sharuddan da majalisar akwai batun sai mukaddashin Shugaban kasa Farfasa Yemi Osinbajo ya amince cewa majalisar na da cikakken hurumin tantance sunayen wadanda gwamnati za ta nada kan wasu mukamai.
A baya Farfesa Osinbajo ya furta cewa ba dole ba ne sai gwamnati ta nemi amincewar majalisa kafin ta nada mutane kan wasu mukamai a lokacin da majalisar ta sake kin tantance Ibrahim Magu.
Wadannan kalamai na mukaddashin shugaban kasar a cewar wasu masu lura da al'amura su suka harzuka majalisar.
Mukaddashin ya yi amfani da fasarar da wani babban lauya Femi Falana ya yi wa wani sashen kudurin dokar kasa kan wannan batu.
Domin jin karin bayani, saurari rahoton daya daga cikin wakilinmu na Abuja Umar Faruk Musa.
Facebook Forum