Mahaukaciyar guguwar teku da aka akawa suna Irene tana ci gaba da hadasawa biranen gabar tekun gabashin Amirka ruwa kamar da bakin kwarya hade da iska mai karfi gaske harma ta kashe akalla mutane hudu ta kuma gurgunta zirga zirgan jiragen sama dana kasa da motocin safa a wasu wuraren.
Da sanyin safiyar jiya asabar ta ratso jihar North Carolina, ta hadasa ambaliyar ruwa da tuge itatuwa, domin kuwa tana tattare da iska ko kuma guguwar dake juyawar kimamin kilomita dari da arba’in cikin sa’a guda. Kusan gidaje da shaguna miliyan daya ne basu da wutar lantarki. Jami’an Amirka sunce mutane uku ta kashe a jihar North Carolina, daya kuma a jihar Virginia.
A birnin New York Magajin gari Micheal Bloomberg ya bada umarnin a kwashe mutane ala tilas daga gidajensu, a wuraren da ake ganin mahaukaciyar guguwar zata fi yiwa barna. Tun kuma misalin karge goma sha biyu na ranar jiya asabar aka dakatar da zirga zirgan jiragen sama dana kasa da kuma bas bas a birnin New York. Mahaukaciyar guguwar teku Irene, itace guguwa ta farko data jawowa Amirka barazana sosai cikin shekaru uku, tun bayan aukuwar Katrina.