An gudanar da bincike ne a kan wadansu ma’aurata daga shekara ta dubu biyu da takwas zuwa dubu biyu da goma a Kenya da Uganda. Daya daga cikin ma’auratan bashi da cutar daya kuma yana da ita.
Binciken ya nuna an sami raguwar hadarin kamuwa da cutar kanjamau tsakanin kashi 67% zuwa 75% na wadanda suka sha maganin kashe kaifin kwayar cutar HIV, idan aka kwatanta da wadanda basu sha maganin ba.
Sai dai ba a sami irin wannan kariyar a bincike na uku da aka gudanar tsakanin mata daga kasashen Kenya da Afrika ta Kudu da Tanzaniya ba.
Binciken da aka buga a mujallar aikin magani da ake New England Journal of Medicine ya bayyana cewa, shan magani ba zai iya maye gurbin amfani da kwararon roba ba.