Tun farko dai ba'a san kan cutar ba da ta lakume mutane a jihar ta Ondo. Bayanin hukumar kiwon lafiya ko WHO shi ya bayyana abun da ka iya zama musabbabin rasa rayukan.
Cutar da tayi sanadiyar mutuwar mutane goma sha takwas ta auku ne a garin Ode-Erinle.
Kakakin hukumar kiwon lafiya ta duniya ko WHO yace gwaje-gwajen da suka yi kawo yanzu, bai nuna kwayar cutar virus ko bacteria ba saboda haka harsashensu shi ne maganin kashe kwari ko na kashe ciyawa ne ya haddasa mutuwar mutanen.
A sanarwar da gwamnatin jihar ta bayar ta tabbatar da mutuwar mutane 18. To saidai rahotannin daga jihar na cewa mutanen garin na ficewa saboda tsoron kamuwa da cutar. Alamun cutar sun hada da zazzabi mai zafi da kuraje da ciwon kai da kuma bushewan gani. Sai kuma mutuwa nan take cikin awa ashirin da hudu.
Barkewar cutar ta sa wasu sun fara tunanen watakila cutar ebola ce. Saidai kwamishanan kiwon lafiya na jihar ya musanta zargin.
Darakta mai kula da lafiyar kan iyakokin kasar Najeriya a ma'aikatar kiwon lafiya ta tarayya Dr. Nasiru Sani Gwarzo yace tuni aka shawo kan cutar. Yace cutar ba irin wadda wanda ya kamu da ita zai iya ba wani ba ce. Ta tsaya kan wadanda ta kama ne. Cutar ba wata sabuwar annoba ba ce wadda zata iya yaduwa zuwa wasu garuruwa. An shawo kanta an kuma fara samun nasara.
Ga rahoton Babanjida Jibrin.