Farfesa Wole Shoyinka ya ce ya zama wajibi a dinga yiwa direbobi gwaji kafin a barsu suna daukan fasinjoji domin gano ko suna cikin hayacin tuka mota.
Wasu direbobin sukan kwankwadi giya, wasu kuma barci bai wadace su ba amma sai su hau hanya da motocinsu da sau tari akan gamu da munanan hadura.
Yanzu dai za’a fara da kafa tasoshi tara a shirin.Wuraren da za’a kafa tasoshin kuwa sun hada da garin Ogbulafor a jihar Enugu da Lokoja a jihar Kogi da Mararrabar Jos a Kaduna da kuma Illela a jihar Sokoto.
Shugaban kungiyar direbobin Najeriya Najim Usman Yasin ya ce suna maraba da tasoshin domin hakan zai taimaka masu suna saurarawa. Yace wurare taran da aka zaba wurare ne da motoci ke tsayawa.
Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi na kan gaba wajen goyon bayan gina tasoshin. Ya ce babbar dabara ce aka kirkiro saboda kungiyar direbobin jiharsa ta fada masa cewa cikin watanni shida ta taba hasarar motoci wajen hamsin da daya da kaya saboda rashin wuraren tsayawa. Yana ganin tasoshin zasu taimaka wurin bunkasa tattalin arziki
Sashen tashar jiragen ruwa ke da alhakin gina tasoshin. A cewar shugaban hukumar jiragen ruwan kusan kashi casa’in na kayan masarufi dake shigowa Najeriya ana rabasu ne ta yin anfani da manyan motoci.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani
Facebook Forum