Ma’aikatan kamfanin hako yurenium a garin Agalik a arewacin Nijar sun dakatar da yajin aikin da suka kwashe kwanaki saba’in suna yi. Kamfanin mallakar kasar Sin ya yi kunne shegu da bukatun ma’aikatan yayin da suka fara yajin aikin. Amma yau sai gashi ma’aikatan da mutanen Sin sun cimma daidaituwa a taron sulhu karkashin shugabancin ministan kwadagon kasar.
Duk abubuwan da ma’aikatan suka nema kamfanin ya yarda ya basu. Idan dai ba’a manta ba kamfanin Faransa dake hako yurenium a garin Arlit ya dakatar da aiki sanadiyar harin kunar bakin wake da aka kai masa makon da ya gabata.
Wakilinmu Abdullahi Mamman Ahmadu ya nada rahoto.