Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma’aikatan Jinya Sun Daina Kulawa Da Masu Corona a Filato


Ma’aikatan jinya da ke kula da wadanda suka harbu da cutar Coronavirus a asibtin koyarwa ta Jami’ar Jos, sun janye daga kula da marasa lafiyan, har sai gwamnati ta samar musu da gidajen da su ma za su killace kansu.

Shugabar kungiyar ma’aikatan jinya da ungozomomi ta kasa, reshen jihar Filato, Madam Briskila Dabit ta ce saboda kusantar marasa lafiyan, har wasu ma’aikatan da ke jinya sun kamu da cutar.

Don haka suke bukatar wurin da za su killace kansu don kar su yada wa iyalansu cutar.

Daraktan asibitin koyarwa a jami’ar Jos, Dakta Edmund Banwat ya ce sun tuntubi kungiyar ma’aikatan jinyan don jin bukatunsu da daukan matakai.

A bangaren gwamnati kuwa kwamishinan lafiya a jihar ta Filato, Dakta Nimkong Ndam ya ce nan ba da dadewa ba za su samarwa ma’aikatan jinyan wurin da za’a rika kebe su.

A cewar hukumar dakile cututtuka a Najeriya NCDC ya zuwa yanzu, mutum 95 ne cutar ta harba a jihar ta Filato, yayin da aka sallami mutum 43 daga asibiti bayan da suka warke.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG