Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikata Fararen Hula Sun Yi Zanga-Zanga Kan Cin Zarafi


Zanga-Zangar kungiyar Ma'aikatan Farar Hula Na Ma'aikatar Tsaro
Zanga-Zangar kungiyar Ma'aikatan Farar Hula Na Ma'aikatar Tsaro

Ma’aikatan farar hula na ma’aikatar tsaro a karkashin inuwar majalisar zartaswa ta hadin gwiwa, sun rufe hedikwatar ma’aikatar da ke Abuja bisa zargin cin zarafin da sojoji suka yi wa mambobinsu.

Shugaban Ma’aikatar na farar hula, Didam Joel, ya ce an tsare wani ma'aikacin farar hula na ma'aikatar har tsawon wata guda a hannun hukumomin soji, duk da cewa shi ba soja ba ne.

Joel ya kara da cewa an kuma ci zarafin wani ma'aikaci mai rike da mukamin mataimakin darakta a ma’aikatar da ke aiki a Makarantar Sakandare ta Command, Ojo, a Legas, a jiya ba tare da bin ka’idojin aikin gwamnati ba.

Duk da dai cewa ya zuwa yanzu rundunar sojin kasar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance game da wannan zargi ba, daya daga cikin Kungiyar Manyan Ma’aikatan Kasar ta Najeriya (ACSSN) a rundunar sojin Najeriya, Abuja, ya bayyanawa manema labarai sunan Ambrose Akhigbe a matsayin wanda aka ci zarafinsa a ranar Litinin da ta gabata .

Ya kuma kara da zargin cewa an kashe wani masanin kimiyar dakin gwaje-gwaje a Asibitin Naval Reference, a Garin Navy, da ke Ojo, a Legas, ‘yan watanni biyu da suka gabata.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG