WASHINGTON, D.C. —
Kungiyar kwallon kafa ta Westham United ta bayyana cewar mai tsaron ragarta Lukasz Fabianski, zai tafi jinya har na tsawon watanni biyu, bayan samun rauni da yayi.
Dan wasan mai shekara 34, da haihuwa ya ji rauni ne lokacin da suke wasa da takwarorunsu Bournemouth, cikin wasan firimiya lig na 2019/20 inda suka tashi 2-2 a ranar Asabar da ta gabata.
Inda Roberto Jimenez mai shekaru 33, ya maye gurbin Fabianski a fafatawa da Bournemouth, kana wannan ne wasan farko da ya buga a firimiya bayan da ya koma West Ham a watan Mayu.
Fabianski shi ne dan wasan da ya fi kwazo a kulob din ganin shine wanda a kakar da ta gabata ya buga wa West Ham United dukkan karawa 38 da ta fafata na firimiya lig din Ingilan.
Facebook Forum