Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool za ta kece raini da takwararta Paris Saint-Germain a daya daga cikin fafatawar da za su dauki hankali azagayen ‘yan 16 na kakar bana ta gasar zakarun nahiyar Turai bayan da jadawalin da aka fitar a yau Juma’a ya hada kungiyoyin.
Karawar farko za ta gudana ne a filin wasa na Parc Des Princes da ke birnin Paris a tsakanin ranaikun 4 da 5 ga watan Maris mai kamawa, inda karawa ta 2 za ta gudana a filin wasa na Anfield bayan mako guda.
Masu rike da kambun gasar Real Madrid za su kara da abokan hamayyarsu na birni Atletico Madrid a maimaicin fafatawar karshe na shekarun 2014 da 2016, wadanda dukkaninsu Los Blancos ce ta samu galaba.
Bayern Munich za ta hadu da abokiyar hamayyarta ta kasar Jamus Bayer Leverkusen, yayin da Arsenal za ta kara da PSV Eindhoven sannan Inter Milan za ta tunkari Feyenoord.
Barcelona za ta barje gumi da Benfica yayin da aston villa za ta hadu da Brugge, ita kuwa Borussia Dortmund za ta hadu da kungiyar Lille ta kasar Faransa.
Dandalin Mu Tattauna