A cikin wani shirin talabijin na shekarar 2017 mai suna "Mata ta Gari," an ga inda likita daga jihar Chicago ta nan Amurka, ya ba da shawara lokacin da ake gabatar da wata tiyata a kasar Siriya, ta kafar bidiyo na Skype.
Irin wadannan ayyukan gaggawa na nesa, wanda likita zai ba da umurnin yadda za’a gabatar da tiyata ga mara lafiya shi ake kira telemedicine a turance, ba kawai kayan almara na talabijin ba ne - fasaha ce da ke jawo hankalin kara daga kasuwanci da gwamnati.
Kasar Singapore, ta bi sahu wajen cin gajiyar fasahar zamanin, inda aka gabatar da dokokin da za su tallafawa shirin na telemedicine, likitoci za su samu damar duba mara lafiya ba tare da ya je asibiti ba.
Kai-tsaye likita zai gana da mara lafiya da yake kwance a gidansa, ta hanyar amfani da bidiyo, sakon gaggawa, da ma waya.
Sai dai tambayar da jama'a da dama ke yi kan wannan sabuwar fasaha ita ce, ko sabuwar fasahar na zuwa tare da wasu haddurra
Akwai batu kamar na sanin kimar daidaitattun likitan-likitoci ta hanyar ganawa ta bidiyo, kuma ya makomar bayanan sirri jama’a, da inshora da kuma tambayoyin alhaki idan aka yi zalunci.
Facebook Forum