Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Likitoci a Najeriya Sun Koma Bakin Aiki


Asibitin National hospital da ke birnin Abuja
Asibitin National hospital da ke birnin Abuja

Likitocin da ke aiki a asibitocin gwamnati a Najeriya sun janye yajin aikin da suka shiga mako daya da ya gabata kan rashin samun isassun kayan kariya, yayin da adadin masu kamuwa da cutar Coronavirus ke karuwa a kasar.

Yajin aikin da gamayyar kungiyoyin likitoci masu kokarin koyon aiki ta (NARD) ta shiga, ya fara ne a ranar 15 na watan Yuni.

Sai dai gamayyar ta baiwa likitocin da ke kula da masu cutar Coronavirus damar su ci gaba da aiki a yayin yajin aikin.

Babban daraktan gamayyar ne ya yanke hukuncin janye yajin aikin daga karfe 8 na safiyar 22 ga watan Yuni.

NARD ta ce matakin ya biyo bayan sa bakin da wasu gwamnoni su ka yi, tare da neman a baiwa gwamnati lokacin biya wa likitocin bukatunsu.

Gamayyar ta fara yajin aikin ne domin rashin isassun kudade da kayan kariya da dai sauransu.

Yajin aikin likitoci dai ba sabon abu bane a Najeriya.

Hoton daya daga cikin cibiyoyin da aka ware domin kula da masu cutar Covid-19 wanda aka dauka jim kadan bayan da likitoci suka janye yajin aiki a cikin watan Mayun shekarar 2020.
Hoton daya daga cikin cibiyoyin da aka ware domin kula da masu cutar Covid-19 wanda aka dauka jim kadan bayan da likitoci suka janye yajin aiki a cikin watan Mayun shekarar 2020.

Hukumomi na fargabar cewa, idan bangaren kiwon lafiya ya fuskanci wani cikas, to iya shawo kan cutar Coronavirus zai iya gagarrarsu.

Ya zuwa yanzu dai mutum fiye da 20,000 ne Suka Kamu da cutar ta Coronavirus a Najeriya.

A cewar hukumar dakile cututtuka a Najeriya ta NCDC, ma'aikatan kiwon lafiya 800 ne suka kamu da cutar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG