Koda yake kokarin jin ta bakin masu gidajen man ya ci tura, inda wasu suka ce suna jiran bayani ne daga uwar kungiyar su ta kasa.
Bincike ya nuna cewar har yanzu akwai layukan ababen hawa a gidajen mai daban daban na birnin Legas da kewaye. Inda babu layi za a taras suna sayarwa ne akan sabon farashin daya haura Naira 500 kowace lita.
A ta bakin shugaban kanfanin matatar mai ta kasa Mele Kyari, matakin da gwamnati ta dauka na janye tallafin ya yi dai dai domin kuwa yanzu gwamnati bata da kudin biyan tallafin da ya haura biliyoyin Naira, don haka muna kira ga gidajen mai su ci gaba da sayar da mai a sabon farashin.
Tuni dai yan Najeriya suka fara maida martani inda wasu suka sheda mani rashin jindadinsu da wannan mataki na sabuwar gwamnatin Bola Tinubu. Wani mutum ya ce gaskiya yanzu ana sayar da mai akan Naira 500 zuwa sama kowace lita daya, da safen nan na saya kuma mutane sun fara gunaguni da sabuwar gwamnatin. Shima wannan malami ya ce kamata ya yi kafin a janye a gyara matatun mai kaman na Dangote a bari ya fara aiki domin haka ne zai kawo sauki ga talaka.
Masana tattalin arziki dai na ganin matakin ya dace kamar yadda Dr. Dauda Mohammed ya ce, matakin zai taimaka wajen ganin a gyara matatun kuma a yi anfanin da kudin wajen gudanar da aikin lafiya da ilimi, ya ce yanzu haka farashin mai yafi araha a Najeriya idan aka kwatanta farashin da kasashe makwabta.
Yanzu dai a yayin da gwamnati ke shirin taro da kungiyar kwadago NLC akan wannan mataki, fatan yan Najeriya shine na samun daidaito na farashin mai yanda za su iya saye.
Saurari rahoton a sauti: