Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lagbaja Ya Zama Cikakken Janaral Mai Tauraro Uku

Lagbaja Ya Zama Cikakken Janaral Mai Tauraro Uku
Lagbaja Ya Zama Cikakken Janaral Mai Tauraro Uku

A ranar litinin din nan ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya karawa babban hafsan sojin kasa, Taoreed Abiodun Lagbaja girma zuwa mukamin LAFTANAR JANAL mai tauraro uku.

Shugaba Tinubu tare da mataimakinsa Kashim Shettima sun makalawa babban hafsan sabon mukamin a kafadar kakin soji, a fadar Gwamnatin kasar ta Aso Rock.

Lagbaja Ya Zama Cikakken Janaral Mai Tauraro Uku
Lagbaja Ya Zama Cikakken Janaral Mai Tauraro Uku

Janar Lagbaja wanda daga bisani ya isa hedkwatar rundunar sojin inda aka gudanar da wata 'yar kwarya-kwaryar liyafa don taya shi murna, ya godewa mayakan kasar, kana ya nemi a kara jan damara don ci gaba da fuskantar kalubalen tsaro a kasar

Sojojin kasar wadanda babban hafsa mai kula da manufofi da tsare-tsare Manjo Janaral Abdulsalam Ibrahim yayi magana a madadinsu, sun yi alkawarin goyon bayan babban hafsan don haka ta cimma ruwa.

Lagbaja Ya Zama Cikakken Janaral Mai Tauraro Uku
Lagbaja Ya Zama Cikakken Janaral Mai Tauraro Uku

Mukamin laftanar Janar dai daya ne kadai ake samu a rundunar mayakan kasa, mai alamar tauraro uku da babban hafsa kadai ake baiwa, yayin da ake kuma samun kwatankwacinsa a rundunar mayakan ruwa da ake kira VICE ADMIRAL da shi ma ke zaman babban hafasan mayakan ruwan, sai kuma kwatankwacinsa a rundunar mayakan sama da ake kira AIR MASHALL, da shi kuma ke zaman babban hafasan sojin sama.

Lagbaja Ya Zama Cikakken Janaral Mai Tauraro Uku
Lagbaja Ya Zama Cikakken Janaral Mai Tauraro Uku

Sai kuma sha kundum, wato shugabansu gaba daya wato mukamin cikakken Janar mai tauraro hudu da ake cewa FOUR STAR GENERAL da ake baiwa babban hafsan hafsoshin tsaron kasa wato CHIEF OF DEFENCE STAFF ko CDS a takaice, da shi kuma shine shugaban hafsoshin baki dayan rundunonin sojojin kasar, na kasa, ruwa da na sama.

wannan mukami dai ana zagayawa da shine tsakanin mayakan kasa, ruwa da na sama.

Lagbaja Ya Zama Cikakken Janaral Mai Tauraro Uku
Lagbaja Ya Zama Cikakken Janaral Mai Tauraro Uku

Cikakken Janaral mai tauraro hudu a sojin sama shi ake cewa AIR CHIEF MASHALL, yayin da cikakken janaral mai tauraro hudu a sojin ruwa shi ake kira ADMIRAL,

Cikin sojin sama masu mukamin babban janar mai tauraro hudu da suka rike mukamin babban hafsa mai tauraro hudu akwai, marigayi Air Chief Marshall Alex Baddeh, a mayakan ruwa kuwa, akwai Admiral Ola Ibrahim.

Amma dai galibi sojojin kasa ne suka fi rike mukamin a tarihi, cikinsu kuwa akwai marigayi Janar Domkat Bali, marigayi Janar sani Abacha, Janar Abdulsalami Abubakar, da Janar Lucky Irabor

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG