Ana rade radin yiwuwar kwararren dan wasan Najeriya Odion Ighalo ya koma Turai idan aka bude kasuwar cafanen ‘yan wasa ta wannan bazara da rahotanni ke cewa tuni wasu kungiyoyi su ka fara zawarcinsa. Tun a kakar wasannin da ta gabata rabon Ighalo ya taka leda a Turai, da kungiyarsa ta lokacin Shinghai Xinhua ta kasar Sin ta ba da shi aro ga kungiyar Manchester United ta Ingila.
To sai dai bayan kammala zama aron, Ighalo ya koma kungiyar Alhilal ta Saudiyya a farkon shekarar nan ta 2022 kodayake ya na da sauran shekara daya a kwantaraginsa da kungiyar, mujallar wasanni ta Skype Sports ta ruwaito cewa kungiyar A.S. Monaco ta kasar Faransa da kuma Getafe da ke fafata LaLiga ta kasar Spain duk sun nuna sha’awar sayen dan wasan a wannan bazara.
Duk dayake kungiyar PSG ta Faransa ta samu tabbacin lashe gasar League 1 ta bana, rahotanni na nuna cewa ta kuduri aniyar sallamar mai horar da ‘yan wasanta Mauricio Pocettino.
A halin da ake ciki kuma, mai tsaron baya a kungiyar Chelsea, Antonio Rudiger zai tafi Real Marid a wani kwantaragi na tsawon shekaru 4.
A bangaren kwallon tennis kuwa, wanda ya fi bajinta a duniya, Novac Djokovic ya gamu da cikas kan batun yin babbar nasara ta farko a shekarar.
Saurari cikakken rahoton Murtala Faruk Sanyinna: