A jamhriyar kwango, gwamnatin kasar ta umarci kamfanonin sadarwa da suke kasar su katse dukkanin hanyoyin sadarwa gobe lahadi, lokacinda kasar take zaben shugaban kasa.
Ministan harkokin cikin gida na kasar Raymond Zephrin, ya aike da wasika zuwa ga manyan kamfanonin sadarwa biyu da suke aiki a kasar cewa, saboda dalilan tsaro, tilas su dakile dukkan hanyoyin sadarwa ciki harda sakon text, a ranakun lahadi da kuma litinin.
Wasikar, wacce aka gani a internet, ta kuma bada jerin lambobi da zasu ci gaba da aiki yayin da ake zaben.
Wannan umarni zai iya kara kara zaman dar dar a kasar, inda mutumin da ya dade yana mulkin kasar, shugaba Denis Sassou Nguesso, yake sake takara, ind a zai kara da wasu 'yan takara takwas, cik harda tsohon hafsa a rundunar mayakan kasar Janar Jean-Marie Makoko.