Mahukuntan Sokoto sun maida hankali ga kawo karshen cecekuncen dake yiwa zaman lafiyar kasar barazana sakamakon martanin da matasan arewa da wasu dattawa suka mayarwa 'yan kabilar Igbo masu hankoron ballewa daga kasar domin su kafa tasu.
A taron da kwamishanan 'yansandan Sokoto Muhammad Abdulkadir ya kira biyo bayan umurnin da shugabansu ya ba duk kwamishanonin 'yansandan jihohin kasar 36 da Abuja, ya shaida masu cewa dukansu 'yan Najeriya ne kuma babu wanda yake da hurumin ya hana wasu ko wani zama cikin kowace jiha ya ga dama.
Taron da kwamishanan ya kira ya hada da duka shugabannin kabilun dake zaune a jihar Sokoto cikinsu ko har da kabilar Igbo dake son ballewa daga Najeriya. Ya fada masu cewa kowa ya kwantar da hankalinsa domin kasancewarsu 'yan Najeriya suna iya zama koina suka ga dama bare da wata tsangwama ba.
Kakakin rundunar 'yansandan ASP Ibrahim Muhammad Abbas yayi karin haske akan taron. Yana mai cewa shugaban 'yansanda na kasa shi ya zauna da kwamishanoninsa ya umurcesu su koma jihohinsu su gana da shugabannin al'ummomin dake cikinsu.
Yace a taron an yi masu bayanin duk matakan da ya kamata a dauka kuma an dauka saboda haka su zauna lafiya lau tare da junansu. Baicin basu tabbacin kare lafiyar kowa, kwamishanan ya basu lambobin wayoyin da zasu iya kira tare da tashi akan abun da zasu yi da zara wani abu na faruwa inda duk suke.
Shi ma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III ya karbi bakuncin shugabannin kabilu mazauna Sokoto da kuma duka shugabannin harkokin tsaro a taron bude baki na daren jiya. Ya gaya masu yakamata a yi la'akari da abubuwan dake faruwa a duniya. Yace babu wanda zai ce yana farin ciki da su.
Ga karin bayani daga rahoton Murtala Faruk Sanyinna.
Facebook Forum