Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamandan Sojojin Sudan ta Kudu da Suka Yiwa Mata Fyade Ya Mutu a Gidan Wakafi


Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir

An samu gawar Luka Akechak kwamandan sojojin Sudan ta Kudu da suka yiwa wasu matana aikin agaji na kasa da kasa fyade a gidan wakafin da yake tsare

Kwamandan sojojin Sudan ta Kudu wanda karkashin kulawarsa ne aka zargi sojoji da laifin kashe wani ‘dan jarida da kuma yiwa a kalla mata ma’aikatan agaji hudu na kasa da kasa fyade a shekarar da ta gabata, ya mutu a cikin gidan wakafinda ake tsare da shi.

Da farko dai an samu gawar Lautanal Luka Akechak, mace a inda ake tsare da shi tun sama da mako guda da ya gabata, amma sai ranar Juma’a aka fitar da rahotan mutuwar.

Kakakin rundunar sojan kasar, Col. Santo Dominic yace ba wata alama dake nuna cewa akwai wata tabargaza wajen kisan nashi.

“Luka Akechak dai ya mutu. Kuma mutuwar ajali ce.” A cewar Domic lokacin da yake magana da Muryar Amurka.

hine babban wanda ake zargi a ta’asar da sojojin Sudan ta Kudu suka aikata, wanda hakan yake nuna yadda yake da matukar wahala wajen gabatar da wadanda ake zargi take hakkin bil Adama ga shari’a a kasar, wacce ta share shekaru hudu tana fama da tashin hankali.

‘Daya daga cikin matan da aka yiwa fyaden ta zargi Akechak da umartar sojojin dake karkashinsa su yiwa mata ma’aikatan agajin fyade a otel din Terrain dake Juba cikin watan Yulin shekarar 2016.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG