Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwalara Ta Kashe Akalla Mutane 33 A Yobe Da Jigawa


cholera
cholera

Rahotanni daga jihohin Yobe da Jigawa sun yi nuni da cewa, barkewar annobar kwalara ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 33 a jihohin biyu.

A jihar Yobe, rahotanni sun bayyana mutane 3 ne suka rasa ransu sakamakon kamuwa da cutar ta kwalara inda wasu mutane biyu ke kwance a asibiti a yankin Girgir da ke karamar hukumar Jakusko a jihar.

Barkewar annobar a jihar Yobe na zuwa ne a cikin kasa da kwanaki 3 bayan da rahotanni daga jihar Jigawa suka bayyana cewa, ana zaton cutar ta kwalara ta yi sanadiyar mutuwar wasu mutane 30 a kananan hukumomin mulki 9 a jihar Jigawa.

Babban sakatare hukumar kiwon lafiya a matakin farko a jihar Yobe, Babagana Kundi Machina, ya bayyana cewa, mutumin farko da ya kamu da cutar ya fito ne daga jihar Jigawa wanda ke makwabtaka da Yobe, lamarin da ya kai ga wasu yan jihar ma suka kamu.

Wadanda suka rasa rayukansu sakamakon fama da kwalara din a jiharJigawa sun sa adadin mutanen da ke mutuwa daga cutar a fadin Najeriya kara yawa.

A halin yanzu dai, sauran jihohin da suka ba da rahoton mutuwar mutane daga cutar kwalara a ‘yan makonnin da suka gabata sun hada da Enugu, Binuwai, Filato, da kuma Bayelsa.

Ya zuwa yanzu, rahotanni sun bayyana cewa mutane sama da dubu biyu ne suka kamu da cutar a jihar Jigawa kadai, ciki har da a babban birnin jihar wato Dutse, inda a karamar hukumar Hadejia ne lamarin ya fi kamari.

A cikin makon nan ma, sai da babban sakataren ma’aikatar lafiya na jihar Jigawa, Salisu Mu’azu, ya dora alhakin yaduwar cutar ta kwalara kan yin bahaya a fili da al’umma ke a yayin zantawa da manema labarai.

Karamar hukumar Jakusko ta jihar Yobe na da iyaka da jihohin Jigawa da Bauchi wadanda a kwanan nan suka yi ta fama da cutar kwalara.

Idan ana iya tunawa, a farko-farkon watan Mayu, akalla mutane 20 suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar kwalara a jihar Bauchi.

Barkewar cutar kwalara a jihar Bauchi ta fi shafar babban birnin jihar wato Bauchi, inda aka samu adadin mutane 147 da suka kamu da cutar a can, daga cikin 322 da aka tabbatar sun kamu da cutar a kananan hukumomin jihar tara.

XS
SM
MD
LG