Wadansu manyan jami’an gwamnatin kasar Kenya sun ajiye mukamansu bayanda kotun bin kadin manyan laifuka ta kasa da kasa tace tilas su gurfana gaban kulliya domin kare kansu bisa zargin cin zaragin bil’adama.
Francis Muthaura zai sauka daga mukamin babban jami’in ma’aikatan gwamnati yayinda Uhuru Kenyatta zai ajiye aikinshi a matsayin ministan kudi, yayinda zai ci gaba da rike mukamin PM.
Kenyatta da Muthaura da tsohon ministan ilimi William Ruto da kuma shugaban wata tashar Radiyo Joshua Arap Sang suna fuskantar tuhuma a gaban kotun bin kadin manyan laifuka ta kasa da kasa ICC sabili da rawar da ake zarginsu da takawa a tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa na shekara ta dubu biyu da bakwai.
Ana zargin mutanen hudu da taimakawa wajen kitsa rikicin kabilancin da ya barke bayan zaben shugaban kasar da aka yi takaddama a kai. An kashe kimanin mutane dubu daya da dari uku yayinda kimanin mutane dubu dari uku suka kauracewa matsugunansu kafin a shawo kan tashin hankalin.
Kenyatta wanda ya kasance shugaban kasar Kenya na farko, kuma daya daga cikin attajiran kasar, ya musanta aikata laifin a wata sanarwa da ya bayar ranar Litinin. Mr. Kenyatta ya bayyana niyarshi ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben da ake kyautata zaton gudanarwa cikin wannan shekarar