Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Rajin Kare Hakkin Bil' Adama Suna Yabawa Najeriya Sabo Da...


Shugaban Najeriya,Dr.Goodluck Ebele Jonathan a bikin faretin kama aiki a sabon wa'adi.
Shugaban Najeriya,Dr.Goodluck Ebele Jonathan a bikin faretin kama aiki a sabon wa'adi.

Gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil-Adama a Najeriya suna yabawa da zartas da dokar samar da bayanai,suna masu cewa wan nan nasara ce wajen kauda kunbiya-kunbiya a harkokin gwamnati.

Gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil-Adama a Najeriya suna yaba da zartas da dokar samar da bayanai, suna masu cewa wan nan nasara ce wajen kauda kunbiya-kunbiya a harkokin gwamnati.

Wani kakakin cibiyar fafutuka da ake kira RKI a takaice yace dokar da shugaba Goodluck Jonatahan ya rattabawa hanu ranar Asabar ta baiwa ‘yan Najeriya damar gano gaskiyar aikace aikacen gwamnati da kuma tabbatar jami’ai da hukumomin gwamnati suna tafiyar da aikinsu kamar yadda doka ta tanadar.

Haka kuma dokar ta bada kariya ga ‘yan fallasa daga ramuwar gayyar hukumomi d a kungiyoyi. Haka kuma wan nan doka ta shafi kungiyoyi ko kamfanonin masu zaman kansu dake samun kudi daga gwamnati ko suke gudanar da aiki a madadin gwamnati.

Wasu kungiyoyin kare hakkkin bil-Adama uku ne suke ta fafutukar ganin an amince da wan nan doka tun lokacinda Najeriya ta koma kan turbar Demokuradiyya a 1999.

XS
SM
MD
LG