Kungiyoyin kwadago sun nemi gwamnmatin tarayya ta rika ware kaso na musamman domin biyan ‘yan kwadago da tsoffin ma’aikata hakkokinsu nan gaba daga tallafin da ta ke baiwa jihohi.
Kungiyoyin kwadagon sun dauki wanna matsaiyar ne biyo bayan jawabin shugaba Muhammadu Buhari ga ‘yan Najeriya albarkacin zagayowar ranar samun ‘yancin kai shekaru hamsin da bakwai da suka gabata inda ya sanar cewa gwamnatin tarayya ta baiwa jihohin tallafi Naira Tiriliyan daya da miliyan dari shida da arba’in da biyu tun hawarsa shugabancin a 2015.
Muryar Amurka ta yi nazarin yadda jihohin Adamawa da Taraba da suka anfana da sama da Naira biliyan goma sha biyar da kuma Naira biliyan takwas ko wannen su amma kawo yanzu ma’aikata ke bin gwamnatocin Adamawa da Taraba albashin watanni hudu zuwa shida musamman ma’aikatan kananan hukumomi, jam’an kiwon lafiya mataki na farko da malaman firamare.
Baki ya zo daya kan kasawar da gwamnatocin suka yi na rage bashin kudin sallama ga tsoffin ma’aikata lokacin da shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya rassan jihohin Adamawa da Taraba Komrad Maina Dauda da Komrad Peter Gambo ke bayanin yadda aka sarrafa tallafin a jihohinsu.
Da yake bayanin abinda ‘ya’yan kungiyarsa suka anfana da shi daga kaso na sama da biliyan sha biyar da gwamnatin jihar ta karba, shugaban kungiyar masu kabar fansho ta kasa reshen jihar Adamawa Komrad Samson Almuru ya ce abin takaici shine domin biliyan daya kacal aka ware don rage bashin tsoffin ma’aikatan gwamnatin jihar da na kananan hukumomi na sama da biliyan ashirin da ta ke bin ta, wanda daga ciki wannan adadin hukumar ta kasa bayanin babu inda Naira miliyan daribiyu da ashirin da bakwai suka yi, sama, ko kasa.
Lokacin da muyar Amurka ta tuntubi shugaban hukumar kula da masu karbar fansho ta jihar Adamawa Alh. Abubakar Njidda Sarau, ya shaidawa wakilinmu Sanusi Adamu cewa gwamnatin jihar Adamawa ta hana shi yi wa ‘yan jarida bayanin yadda hukumarsa ke sarrafa kudade da ke shiga asusun ta.
Facebook Forum