WASHINGTON, DC —
Wasu kungiyoyin fararen hula sun kira taron gangami dagane da kin amincewarsu da yadda ake gudanar da mulkin kasar.
A yayin taron gangamin sun gabatar da korafe-korafe da dama wadanda suke gani su ne suke son maida hannu agogo baya a harkokin kasar. Akwai batun cin hanci da rashawa da rashin kiwon lafiya da kungiyoyin suka ce sun gurbace tun da wannan gwamnatin ta hau karagar milki kusan shekaru biyu da rabi ke nan.
Malam Sirajo Isa jagoran kungoyoyin fararen hula ya ce akwai cin hanci da rashawa da rashin adalci da zalunci da milki irin na Firauna da tabarbarewar ilimi da kiwon lafiya su ne umalubaisan abubuwan dake wakana a kasar Niger. Shugaban kasar ya kasa kare rantsuwar da ya yi yayin da yake kama aiki.Ya yi alkawarin yin aiki da zai fitar da duk wani dan Niger daga talauci da tsadar rayuwa to amma ba haka lamarin yake ba a yanzu.
Taron gangami ya zo ne daidai lokacin da kasar ta Niger ke fuskantar wani rudanin siyasa. A kowane mako ko wasu su fito suna yabawa gwamnati ko kuma wasu su fito suna ma gwamnatin tofin alatsine.
Yayin da yake mayar da martani a taronsa da manema labarai Malam Asma Muhammadu daya daga cikin jigajigan kungiyar siyasa dake mulkin kasar ya ce ba'a taba samun gwamnatin da ta yi irin aikin da gwamnati mai ci yanzu ta yi ba cikin shekaru biyu da rabi. Ya ce abun da aka yi yau da gwamnatocin da suka shude sun yi hakan da babu korafe-korafe ko guda. Ya ce a garuruwa babu inda aka gina makaranta daya sai uku kuma a kammalasu. Ya ce to amma da yake sun samu kasa kwance wadanda suka saba da cin hanci da rashawa dole su shiga yin korafe-korafe. In ji shi, wadannan abubuwa ba zasu tada masu hankali ba.
To sai dai kungiyoyin da suka shirya gangamin sun ce sai sun tilstawa gwamnati ta dawo kan hanya duk da wai wasu 'yan kasa suna yima gwamnatin guda domin tun da gwamnatin ta zo suka shiga wata aljannar duniya.
Ga rahoton Abdullahi Mamman Ahmadu.