Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Zabgai International dake Jihar Bauchi a tarayyan Najeriya, Alhaji Babangida Yalwa Jahun, ya bayyana bukatar kulob din ga masu hannu da shuni da kuma masu sha’awar harkar kwallon kafa da su taimaka domin ganin wannan kungiya ta cigaba da samun nasarori.
Kungiyar ta Zabgai kungiya ce mai dinbin tarihi wace take taimakawa matasa a jihar Bauchi dama kasa baki daya ta bangaren wasanni.
A shekarar 2018 Zabgai ta kasance wace ta lashe gasar cin kofin kalu bale na Jihar Bauchi, bayan da ta samu basara akan Wikki Tourist, inda ta wakilci jihar a gasar ta kasa bayan haka kuma a 2019, kungiyar ta kare a mataki na biyu.
Babangida Yalwa, yaci gaba da cewar tun da aka kafa kungiyar a shekarar 1976, kimanin shekaru 43, akwai manyan 'yan jihar ta Bauchi da suke taimaka mata Irin su Marigayi Maimartaba Sarkin Bauchi Dr Suleman Adamu da Marigayi Sabo Adamu Jumba, Marigayi Isa Yalwa, Marigayi Uban Doman Jama’are.
Sau ran masu tallafa wa kungiyar Sun hada da Alh Isa Musa Matori, da Alhaji Abdullahi Matori, da Alh Jumba Fali, Altine Killer, Comr Abdullahi Ibrahim Askiya, da dai sauran su.
Shugaban yace har yanzu kungiyar tana bukatar taimako kama daga wajen dai-dai kun al'umma da kamfanoni.
Daga karshe yayi alkawarin cewa kungiyar zata cigaba da kawo nasarori a bangaren wasanni wa jihar da ma kasa baki daya.
Facebook Forum