Gamayyar Kungiyoyin Arewa CNG ta mayar da martani ga haramtacciyar kungiyar ‘yan asalin Biafra, IPOB bisa umarnin ta na haramta cin naman shanu na Fulani a yankin Kudu maso Gabas, inda ta yi kira da a kaurace wa duk wani kasuwancin da ‘yan kabilar Igbo ke gudanar da su a duk fadin yankin Arewa.
CNG ta bakin mai magana da yawunta Abdul-Azeez Suleiman ya bayyana cewa, umurnin na IPOB na kunshe ne cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin da ya ba da umarni ga mutanen yankin da su daina cin naman shanun da yan arewa suka kai yanki daga ranar 8 ga watan Afirilun 2022.
Wannan Lamari ya kasance babban tsokana da babbar barazana ga sha’anin kasuwancin Arewa a yankin Kudu maso Gabas da kuma ci gaban rayuwar ‘yan Arewa mazauna yankin, wadanda suka kasance tsiraru a cikin al'ummar Igbo a cewar Abdul-Azeez Suleiman a wata hira da Muryar Amurka ta yida shi
Ya kuma kara da ce dalilin hakan ya sa kungiyar daukar matakin yin barazana na kauracewa dukkan kasuwanci da Ibo ke yi a fadin yankin arewacin Najeriya.
ya ce tabbas wannan sanarwa ta fusata su kuma babbar barazana ce ga kasuwancin arewa a kudu maso gabas da kuma 'yan arewa da ke zama a yankunan Ibo.
"A kokarin ganin an shawo kan duk wata barazana kai tsaye ko a kaikaice ga 'yan arewa a ko ina a kasar nan, CNG na kira kan kauracewa dukkan kasuwan, kayayyaki da Ibo ke siyarwa a watan Afirilu. “CNG ta yi kira ga 'yan arewa da ke ko ina da su daina nuna goyon baya ga jam'iyyar siyasa da kungiyoyi da ke kudu maso gabas tare da 'yan siyasar su.
“Domin kore shakka, arewa yayin kiyaye al'adarta ta hakuri da juriya, ba za ta ci gaba da lamintar kowanne irin barazana da hantara ba da aka yi domin dakile halastattun kasuwancin 'yan arewa a kowanne sashi na kasar nan a cewar sa.