Hukumar kula da wasan kwallon kafa ta duniya FIFA tare da na tarayyar Najeriya NFF, sun jera sahu guda wajan taya tsohon dan wasan Najeriya Finidi George, murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
A ranar Litinin 15 ga watan Afirilu 2019 ne tsohon dan wasan na Ajax da Real Betis din ya cika shekaru 48 a duniya.
Inda suma kungiyoyin Real Betis, da Ajax ba'a barsu a baya ba wajen taya tsohon dan wasan gefe Finidi George, murnar zagayowar ranar haihuwa warsa.
Dan wasan a lokacin yana fafata wasa kafin ya ajiye takalman wasansa, ya buga wasanni har guda 62 wa tawagar kungiyar kwallon na Super Eagles ta kasarsa Najeriya.
Cikin nasarorin da Finidi ya samu a lokacin ya samu nasarar lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka a shekara 1994, da aka buga a Tunisiya, bayan haka yana daya daga cikin tawagar 'yan kwallon Najeriya da suka fafata a gasar cin kofin duniya na 1994 a Amurka, da kuma wanda akayi a kasar Faransa shekara ta 1998.
Bayan haka kuma ya samu nasarar lashe kofin Zakarun Turai UEFA Champion League, tare da tawagar kungiyar kwallon kafa ta Ajax, a shekara ta 1995.
Facebook Forum