Dan wasan baya na gefen dama dake buga wa kungiyar kwallon kafa ta Jigawa Golden Star, a tarayyar Najeriya mai suna Bilal Yakubu, wanda aka fi sani da (Bilal Gunji) ya zubar da hawayensa saboda murna bayan da aka tashi daga wasan da suka buga da kulob din Wikki Tourist na garin Bauchi cikin gasar NPFL, na 2019/20, makon farko.
Wasan ya guda nane a filin wasa na Pantami dake jihar Gombe inda aka tashi a wasan Wikki tayi nasara da ci 2 da 1.
Bilal Gunji, wanda dan asalin jihar Bauchi ne ya fara buga wasansa a kungiyar matasa mai suna 3SC FC, kar kashin jagorancin Safiyanu Chelaverd, yayi wasansa a Yankari Babies, da kuma Wikki Feeder inda daga bisani ya koma kungiyar kwallon kafa ta Jigawa Golden Star, wacce ta hauro gasar firimiya lig na Najeriya a bana.
Dan wasan dan shekaru 19 da haihuwa ya bayyana dalilin zubar da hawayensa, a yayinda suka buga da kungiyar ta Wikki wadda ta fito daga mahaifarsa, yace matasa sun nuna masa kauna domin sun tashi tun daga jihar Bauchi har jihar Gombe kimanin kilomita 130, suka nuna masa goyon baya, hakan ya nuna masa tsantsan kauna dake tsakanin sa da 'yan uwansa.
Ita ma anata gefen kungiyar ta Jigawa Golden Star ta karrama dan wasan, inda ta bashi kambun jagorancin 'yan wasan (Captain) a yayin wasan na ranar Lahadi.
Jigawa Golden Star sune suka fara jefa kwallo a ragar mai masaukin baki ta kafar dan wasanta Abdullahi Musa, kafin tafiya hutun rabin lokaci daga bisa Wikki ta farke ta kara ta hannun dan wasanta Sa'idu Abdullahi Yellow, da Alhaji Guda haka aka tashi a wasan 2-1.
Daga karshe Bilal yayi godiya bisa karamci da aka nuna masa daga bangaren 'yan uwansa na Bauchi dama kungiyar tasa. A wasan mako na biyu kuwa cikin gasar NPFL Jigawa zata karbi bakoncin Plateau United.
Facebook Forum