Kungiyar kwallon kafa ta VOA Hausa Flamingos FC Bauchi ta lashe kofin Super League na Jihar Bauchi na wannan shekara ta 2011 a bayan da ta zamo zakara a tsakanin kungiyoyin kwallon kafa 24 da suka shiga cikin wannan gasar a bana.
A wasan karshe da aka buga ranar asabar din nan a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi, kungiyar ta VOA Hausa Flamingos FC ta doke Super Starlets FC Azare da ci 1-0.
Kafin ta zo ga wannan matsayin na wasan karshe, kungiyar VOA Hausa Flamingos ta zamo zakara a rukunin A wanda ya kunshi kungiyoyi 6, daga yankin Bauchi. A bayan da ta lashe rukunin ne sai kungiyar ta doke Beacon FC Tilde a bugun fenariti a wasan kusa da karshe.
Manyan bakin da suka kalli wannan wasa sun hada da tsohon sakataren Hukumar Kwallon kafa ta Najeriya, Alhaji Sani Ahmed Toro, da shugaban kungiyar Wikki Tourists, Sule Tiger, da darektan Hukumar Kwallon kafar Jihar Bauchi, Haruna Bako, da mai bayarda shawara kan wasan matasa ga Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya, Pascal Patrick.
manyan bakin sun yaba ma kungiyar VOA Hausa Flamingos a saboda irin bajimtar da ta nuna wajen lashe wannan kofi.