Jakadar Tarayyar Turai a Najeriya Samuela Isopi ce ta bayyana hakan a yayin jawabinta a taron manema labarai kan murnar ranar tarayyar turai ta shekarar 2022.
Haka kuma, Isopi tace kungiyar EU na ganin darajar Najeriya, ta na mai cewa a nahiyar Afurka ita ce kasar da kasashen Turai suka fi hulda da ita da hakan ke nuna muhimmancin kasar a duniya.
A cewar Samuela Isopi, Tarayyar Turai zata cigaba da tallafawa Najeriya wajen shawo kan matsalolin dake addabarta musamman a bangaren tsaro, ilimi, kiwon lafiya da kuma kare faruwar karancin abinci da kan kai ga kasar fuskantan fari.
Isopi ta kuma ce Najeriya na daga cikin kasashen dake da iskar gas mai dimbin yawa a duniya kuma a shirye kasashen turai su ke su kulla alakar cinikayya ta fuskar cimma yarjejeniya don bangarorin biyu su karu da juna ta fuskan bunkasa tattalin arziki.
Kamar yadda tarayyar turan ta nuna Najeriya ke samar da kaso 39 cikin 100 na iskar gas da kasashenta suke samu daga kasashen duniya.
Rahotanni daga kungiyar ta EU sun yi nuni da cewa tun shekarar 2015 EU din ta bada tallafin Euro miliyan 120 contribute ga Najeriya da sauran kayayyakin tallafi.