Kungiyar ta 'yan bindigan ko NDA ta sanar da kai jerin hare-hare a shafinta na yanar gizo.
Kungiyar tace ta kai hari akan tashar man kamfanin Chevron na kasar Amurka da kuma kamfanin NNPC mallakar gwamnatin Najeriya. Kamfanonin su kan tura dayan mai zuwa tashar Warri dake jihar Delta. Tsakanin Asabar da jiya Lahadi kungiyar tace ta kai hare-hare har sau hudu, kuma tayi nasarar lalata bututan mai.
Janar Rabe Abubakar mai magana da yawun rundunar sojan Najeriya ya yi magana akan hare-haren. Yace a matsayinsu na jami'an tsaro dole ne su dauki matakan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Akan zargin da ake yiwa sojoji wai suna jan kafa, Janar Abubakar yace suna aiki da bin dokoki ne. Ba zasu wuce abun da shugabaninsu suka gindiya masu ba. Amma sojoji suna daukan matakan da suka dace domin kawo karshen tashin tashinar.
Ga karin bayani.