Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Malaman Kwalajojin Kimiya da Fasaha ta Lashi Takobin Cigaba da Yajin Aiki


Dalibai suna zanga zanga
Dalibai suna zanga zanga

Kwana kwanan nan malaman jami'a a Najeriya suka dawo daga yajin aikinda suka fantsama ciki har na tsawon watanni biyar da 'yan kai sai gashi takwarorinsu na kwalajojin kimiya da fasaha sun fara nasu.

Kungiyar malaman kwalajojin kimiya da fasaha ko ASUP a takaice ta ce babu gudu babu ja da baya a yajin aikin da ta shiga sai an biya mata bukatunta.

A wani taron manema labarai da kungiyar ta kira a Kaduna, matamakin shugaban kungiyar na kasa Malam Usman Yusuf Dutse ya ce ba zasu dakatar da yajin aikin ba sai gwamnatin tarayya ta cika alkawuran da ta yiwa kungiyar. Ya ce gwamnatin tarayya ta nuna halin ko inkula game da ilimin kimiya da fsaha a Najeriya. Yajin aikin da suke yi kokari ne na kawo gyara wanda baya yiwuwa sai an ji jiki. Domin haka yana kiran iyaye su yi hakuri haka ma suma daliban su yi hakuri. Idan sun dawo za'a ga canji da yaddar Allah.

Suna da bukatu a gaban gwamnati da yawa. Sun kai wajen goma sha uku. Akwai yarjejeniyar da suka yi da gwamnati tun 2009 kuma a cikinsu babu wanda gwamnati ta cika. Kullum sai su bada hakuri har aka zo 2013 suka kuma bada hakuri da alkawarin cewa su zabi guda hudu da suka ce zasu yi.Sun yi alkawarin cika hudun cikin sati biyu amma basu yi ba. An basu wata daya, biyu har shekara basu yi ba. Dalili ke nan kungiyar ta koma yajin aiki.

Idan zasu cika hudun malaman zasu koma bakin aiki.To saidai bisa ga la'akari da yadda gwamnatin yanzu ke aiki bata damu da ilimi ba. Cikin kasashe 30 na Afirka da UNESCO ta bincikesu kan harkokin ilimi Najeriya ita ce ta zo karshe. Kananan kasashe kamar su Liberia da Togo da makamantansu sun fi Najeriya. A kasafin kudi yayin da wasu kasashe ke bada kashi 30 ga harkokin ilimi, Najeriya kashi 8 take bayarwa. Lokacin gwamnatin Abacha ne kadai aka taba bada kashi goma sha daya.

Abun da ya kama daga dakunan karatu da na kwana da kayan aiki irin wadanda an ma daina anfani da su duk sun lalace sun shude. Babu yadda za'a cigaba da tafiya haka. Dole a kawo canji.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Shiga Kai Tsaye
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG