Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Makiyaya Miyetti Allah ta karyata cewa tana shirin kai harin fansa a Mambila


:Gwamnan Taraba Darius Isyaku yayinda yake ganawa da Shugaba Muhammad Buhari
:Gwamnan Taraba Darius Isyaku yayinda yake ganawa da Shugaba Muhammad Buhari

Ziyarar da gwamnan Taraba ya kaiwa Shugaba Muhammad Buhari ta sa kungiyar Fulani, Miyetti Allah, cewa gwamnan yana neman karin jami’an tsaro ne wai domin ya dakile duk wani yunkurin daukar fansa da Fulani zasu yi lamarin da suka musanta.

Hadakar kungiyar Fulani makiyaya ta najeriya, Miyetti Allah ta karyata rahotannin cewa Fulani makiyaya sun raba goron kai harin fansa a yankin Mambila dake jihar Taraba arewa maso gabashin Najeriya don rama barnar da aka yiwa makiyayan a kwanakin baya.

Wannan dai ya biyo bayan ziyarar da gwamnan jihar Taraba Arch. Darius Dickson Ishaku ya kaiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari inda gwamnan ya nemi a turo masa sojoji don hana daukan fansan, batun da gwamnan ke cewa ba haka zancen yake ba.

Hadakar kungiyar makiyaya a wani taron manema labarai ta musanta wannan zargi tare da nuna bacin ransu gami da cewa watanni hudu bayan tashin hankalin, ya zuwa yanzu ba’a damke wadanda ke da hannu a tashin hankalin ba.

Shugabanin Fulani makiyayan karkashin inuwar Miyetti Allah, sun yi fatali da zargin cewa akwai yuwuwar daukan fansa, inda koma suka nuna mamakinsu da gwamnan ne a yanzu ke neman a tura sojoji jihar.

Sahabi Mahmud Tukur shine shugaban kungiyar ta Miyetti Allah a jihar yace,da walaki, wai goro a cikin miya a wannan bukatar da gwamnan ya mika, musamman a wannan lokaci da ake haramar soma aiki da dokar hana kiwo a jihar.

Tun farko dai shugaban kungiyar miyetti Allahn mai kula da jihohin arewa maso gabas, Mafindi Umaru Danburam yace abun takaici ne abubuwan dake faruwa a jihar, musamman batun dokar hana kiwo da yace ba zata haifar da da mai ido ba.

To sai dai da yake maida martani gwamnan jihar Taraban Arch.Darius Dickson Isiyaku ta bakin hadiminsa ta fuskacin harkokin yada labarai Mr Bala Dan Abu, yace ai ba’a fahimce shi ba ne, domin ko ya nemi a turo sojojin ne don tabbatar da tsaro a jihar ba wai don cin zarafi, ko musgunawa wani ko wasu ba.

Mr. Bala Dan Abu yace, mai girma gwamna mutun ne mai son zaman lafiya, kuma ya roki karin jami’an tsaron ne don kara wanzar da zaman lafiya, ba wai cin mutuncin wani ko wasu ba.

Ta yaya mutumin dake son zaman lafiyan, za’a ce zai kawo sojoji domin a musgunawa jama’arsa, ai ba shine babban kwamandan askarawa ba,’’ inji shi.

A watan Janairu na shekara mai zuwa ne ake sa ran soma aiwatar da sabuwar dokar, da ke ci gaba da jawo cacar baki.

Ga Ibrahim Abdulaziz da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG