WASHINGTON, DC —
Kungiyar Majalisar Dattawan Arewa ta yi taro a Kaduna inda ta yi kokarin musanta zargin cewa an kafata ne domin yiwa shugaban kasar Najeriya Jonathan yakin neman zabe na shekarar 2015.
Kungiyar ta yi fatali da zargin cewa manufarta ita ce ta yi tallar shugaba Goodluck Jonathan a zabe mai zuwa. Da yake amsa tambayoyi jim kadan bayan kammala taro kungiyar jiya a Kaduna shugaban kungiyar Alhaji Tanko Yakasai ya ce idan har maganar tallar Jonathan ce to kungiyar nada baki. Ya ce an kafa kungiyar ne domin sun ga alama ana son a kawo tashin hankali a kasar amma su basu yadda da tashin hankali ba. Kullum addu'ar sarakuna ita ce Allah Ya bamu zaman lafiya kuma kasar ta kasance cikin zaman lafiya.
Dangane da cewa kungiyar tamkar kishiya ce ga kungiyar tuntubar juna ta dattawan arewa ko ACF a takaice sai Alhaji Yakasai ya ce an kafa ACF wajen shekaru 12 amma shi da Alhaji Ali Mongunu ne kadai suka rage a kungiyar. Ya kuma bada tarihin kungiyoyi da aka sha kafawa tun lokacin Janaral Hassan Usman Katsina.
Shi kuwa yariman Muri Alhaji Tafida Isa Mafindi ya ce kungiyar an kirkirota ne domin tattara duk matsalolin arewa su mikawa duk wanda ya ke so ya yi takara. Ya ce sun duba sun ga suna da abubuwa da yawa da yakamata su fitar su ce su ne bukatun arewa. A yanzu babu wata kungiya daya da zata iya tallata bukatun kuma su karbu a lokacin da ya kamata. Kan Jonathan kuwa ya ce ba niyarsu ba ke nan. Ya ce basa tafiya da jam'iyya guda. Ya ce yanzu zasu fitar da bukatun arewa ne. Duk mai tafiya APC ya tafi da bukatun arewa haka ma duk mai tafiya PDP.
Amma shugaban hada kan al'ummar arewa Alhaji Adamu Aliyu ya ce kungiyar ba maganar arewa ce a gabanta ba. Ya ce duk wani dan arewa na kirki ba zai yi murna da taron kungiyar majalisar dattawan arewa ba. Ya ce kodayake suna kiran kansu dattawan arewa dattaku bai yadda da irin abun da suke yi ba.