Wasikar da suka rubuta wacce daraktan bincike na kungiyar ya sanyawa hannu ta bayyana kungiyar da Ibrahim El-zakzaky ke yiwa jagoranci a matsayin 'yan tawayen da Iraniyawa ke mara wa baya.
Idan ba'a manta ba cikin 'yan kwanakin nan Amurka ta fito karara ta nuna rashin jin dadinta dangane da yadda jami'an tsaron Nakeriya ke yiwa kungiyar diran mikiya.
Lauyoyin suka ce maimakon Amurka tace ana afkawa 'yan kungiyar Shi'a ta Ibrahim El-zakzaky su 'yan Shi'a din ne ma ke afkawa 'yan Najeriya saboda basa bin dokokin kasa. Lauyoyin sun kira gamnatin Amurka da ta saka Islamic Movement of Nigeria ('Yan Shi'a) cikin ayarin kungiyoyin 'yan ta'ada.
Baicin ofishin jakadancin Amurka lauyoyin sun mika wasikar kokensu ga ofishin jakadancin Jamus da na Majalisar Dinkin Duniya dake Abuja, babban birnin Najeriya.
Malam Sha'aibu Ahmed shugaban sashen malamai da dalibai na kungiyar Shi'a ta Ibrahim El-zakzaky ko Islamic Movement of Nigeria yace shi bai san abun da lauyoyin ke nufi ba. Idan lauyoyin suka ce a sanya kungiyarsu cikin ayarin kungiyoyin ta'adanci yace shi bai san ta'adancin da su keyi ba. Shi ya dauka kungiyar lauyoyin zata matsa lamba ne akan yakan kungiyar Boko Haram da kashe-kashen da a keyi a Najeriya.
Dr. Abubakar Muazu wani malami a jami'ar Maiduguri yace 'yan Shi'a suna da dama su yi addininsu ba tare da sai sun musgunawa kowa ba. Kuma dole ne su san cewa kasar Najeriya tana da dokoki kuma dole ne a darajasu. Yace kamar yadda lauyoyin suka yi bayani, idan mutum yana jin shi yana da hakki to wani ma yana da nashi hakkin. Yace dole ne su goyi bayan doka domin dokar bata hanasu yin addininsu ba.. Yace kamar abun da suka yi a Zaria inda suka hana hafsan sojoji wucewa har aka kaiga kashe kashe babu dadi.
Inji Dr Muazu kungiyar lauyoyi stana da gaskiya saboda maganar da lauyoyin su keyi domin a kare hakkin kowa ne.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.