.
Kungiyar Kwallon Kafar Mata ta Amurka Ta Buge Jamus
Kungiyar Kwallon Kafar Mata ta Amurka ta doke kasar Jamus da 2-0 a wasan kusa da karshe a birnin Montreal dake kasar Kanada, a gasar kofin kwallon kafa na duniya. Za'a yi wasan karshe a birnin Vancouver. 30 ga watan Yuni, 2015

5
Magoya bayan Amurka suna murnar nasarar buge Jamus a wasan kusa da karshe a gasar kofin duniya na mata a kasar Kanada. 30 ga watan Yuni, 2015

6
'Yar wasan Amurka Kelley O'Hara (5) tana wasa tare da Nadine Angerer (1) na Jamus a wasan FIFA na mata a filin kwallon Olympique, 30 ga watan Yuni, 2015 a birnin Montréal, Québec.

7
Abby Wambach (20) ta Amurka tana murnar samun nasara akan kasar Jamus da (2-0) a gasar FIFA na wannan shekara a kasar Jamus. 30 ga watan Yuni, 2015.

8
'Yar wasan Amurka Alex Morgan (13) da abokiyar wasa Saskia Bartusiak (3) a gasar kofin duniya na kwallon kafar mata (FIFA) a kasar Kanada. 30 ga watan Yuni, 2015