Duk da rawar gani da kungiyar kwallon kafa ta mata a Afrika ta Kudu Bayana Bayana ke takawa, kungiyar bata samun tallafi, bacin wanda take samu daga wani kamfani daya tsawon shekaru goma yana tallafa mata, yanzu da kungiyar ta kai ga shiga gasar cikin kofin duniya. Ya kamata a sauya al’amura indai muna so kungiyar ta kara samun nasara, inji wani kwamitin majalisar dokoki.
A daidai wannan lokaci da shigar Bayana Bayana a gasar cin kofin duniyar a Faransa a cikin watan Yuni ke kara matsowa, har yanzu kungiyar ta mata na ci gaba da fama da tsohuwar matsalarata ta rashin samun tallafi.
Da yake bada bahasi a gaban majalisa, shugaban hukumar kwallon kafar Afrika ta Kudu mai rikon kwarya Russell Paul, yace ba zamu samu ci gaban kwallon mata a cikin kasar ba har sai an samu tallafi kuma ana bukatar tallafin ga kungiyar mata.
Paul da wasu manyan hukumar kwallon kafar sun bada bahasi a gaban majalisar dokoki a kan irin halin da kungiyar mata ta Bayana Bayana ke ciki da kuma irin shirye shirye da take yi kafin fara gasar cin kofin duniya a cikin watannin Yuni da Yuli.
Ya bayyana a cikin bada bahasin ga majalisa cewa baicin kudin kasar R20-million wanda ya yi daidai da dala miliyan daya da dubu dari biyar da ta samu domin shirye shiryen shiga gasar duniyar, kungiyar tana bukatar tallafi mai yawa.
Facebook Forum