A Jamhuriyar Nijar, an kafawa 'yan gudun hijrar Najeriya da fakewa a yankin Diffa makaranta domin a ilimantar da su.
Wata mata da ta fito daga Kenya ita ce ta kafa makarantar tare da hadin gwuiwar wata hukumar Majalisar Dinkin Duniya domin samar ma 'ya'yan 'yan Najeriya dake gudun hijira a Diffa cikin kasar Jamhuriyar Nijar ilimi.
An kafa makarantar ne a shekarar 2014 kuma darusan da ake koyaswa basu da banbanci da na da can.
Abun takaici shi ne yadda gwamnatin Najeriya bata kula da makarantar ba kogayake hukumomin ilmin Nijar suna kai ziyara su bada shawarwarin gyara wasu kurakurai. Baicin shawarwari babu abun da ita ma gwamnatin Nijar din take bayarwa.
A saurari cikakken rahoton Tamar Abari.
Facebook Forum