Wannan yunkuri na kungiyar nada nasaba da cusa akida mai kyau ga al’ummar musulmi, biyo bayan nasarar da gwamnatin Najeriya, ta cimma na dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, da kuma nasarar da zata inganta wajan ci gaba da wa’azi, da kafa makarantu da kuma sauran cibiyoyin da zasu rika ilimantar da al’umma akan addinin musulunci da kuma ilimin zamani.
Kungiyar ta gudanar da wani gagarumin wa’azi a birnin tarayya Abuja, domin karfafa wannana kuduri da kuma manufa kamar yadda shugaban majalisar malamai na kungiyar a Abuja, Ustaz Ibrahim Duguri, ya bayyana.
Mai wa’azi na kungiyar sheik Bashir Kashere, ya karfafa ayyukan kungiyar na marawa neman ilimi baya.
Kungiyar ta yi amfani da wannan dama wajan kira ga majalisun dattawan Najeriya, da su rika mayar da hankali wajan abubuwan da suka shafi kasa kamar yadda sheik Sani Yahaya Jingir, shugaban majalisar malaman kungiyar na kasa ya yi Karin bayani.
Daga karshe kungiyar ta kaddamar da littafi mai taken Boko Halal, dake karfafawa mutane gwiwa wajan neman ilimi da cire tsoron ‘yan ta’adda dake hana al’umma sukunin neman abin tallafawa ta hanyoyin halal.
Hassan Maina Kaina nada Karin bayani.
Facebook Forum