Wani faifan bidiyon farfaganda da kungiyar ta'addanci ta ISIS ta fitar ya nuna kwanton baunar da aka yi a Nijar har aka kashe sojojin Amurka hudu bara.
Faifan bidiyon ya nuna lokacin da aka kaiwa Amurkawan hari. Sojojin ba su da isassun makaman da zasu tunkari dumbin mayakan dake dauke da bindigogin da ake sabawa a kafada, da gurneti. Bisa ga dukkan alamu wani bangaren bidiyon mai tsawon kusan minti tara, an dauke shi ne da kyamarar daukar hoto da ake makalawa a hular kwano ta daya daga cikin sojojin da aka kashe. Wannan bangaren hoton bidiyon ya nuna wadansu sojoji guda biyu suna harbi suna gudu gefen wata mota yayinda ake harbinsu kusa da kauyen Tongo Tongo.
Bidiyon ya kare a inda sojan dake dauke da kyamarar ya fadi, yayin da aka ga mayakan ISIS sun zo sun kewaye shi, suka kuma harbe shi.
Ma’aikatar tsaron Amurka ta fada jiya Litinin cewa, tana sane da faifan bidiyon. Tace, “fitar da faifan bidiyon ya nuna irin rashin imanin makiyan da muke yaki da su.”
Kwanton baunar da aka yi ranar hudu ga watan Oktoba shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai, ya sa ma’aikatar tsaron Amurka gudanar da bincike domin sanin ko sojojin sun sami horaswar da ta kamata, da ko suna da makaman gudanar da aiki a kasar dake yammacin Afrika. Ana kyautata zaton za a fitar da sakamakon binciken cikin wannan watan.
Facebook Forum