Kungiyar kwallon kafa ta Gombe United da ke tarayyar Najeriya, ta dauki Aliyu Zubairu a matsayin sabon maihoras da kungiyar a kakar wasan 2019/20 zuwa 2021.
Aliyu Zubairu dai a hukumance ya rattaba hannu bisa kwantirakin shekaru biyu. An gudanar da bukin kaddamar da shine a filin wasa na Pantami dake garin Gombe.
Aliyu wanda haifeffen jihar Kwara ne kafin zuwan sa shine tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourist, dake Bauchi wacce makwabciyar Jihar Gombe ce.
Tun a ranar Asabar 12 ga watan Oktoban da muke ciki, Aliyu ya ajiye aikinsa da Wikki sabo da wasu dalilai na kashin kansa.
Kocin yayi alkawarin dawo da martabar kungiyar ta Gombe United, wacce zata buga gasar kasa da Firimiyan Najeriya NNL 2019/20. Ya kuma bukaci Gwamnatin jiha, 'yan wasa da al'ummah su bashi dukkannin goyan baya da zai bukata.
A nashi jawabin Shugaban kungiyar Alh Sule Musa (Jasper) ya tabbatar wa sabon kocin tare da tawagarsa na koyar da fasaha (Technical Crew) samu dukkanin goyan bayan hukumar don samun nasara a kakar wasanni.
Cikin wadanda suka halarci bikin sun hada da Alh Abubakar Yellow wanda mamba ne a hukumar gudanarwa na kungiyar ta Gombe United.
Facebook Forum