A wata ziyara da kungiyar ta kaiwa sarkin Irigwe a karamar hukumar Bassa ta jihar Filato, shugaban kungiyar Rebaran Aliyu Buba ya ce zasu ci gaba da yin addu’a da nemo dabarun zaman lafiya tare da yin sulhu tsakanin Fulani da sauran kabilu a Najeriya.
Rebaran Aliyu Buba yace suna son su nunawa duniya cewa akwai Fulani da basa cikin irin ayyukan da wasu su keyi. Ya fada cewa babu mutumin da zai zubar da jinin wani da zai shiga aljanna kowane addini yake.
Yayi kira ga gwamnati data karantar da kowane Bafullatani a duka inda yake domin su sani cewa zamanin da ake ciki yanzu ba na fada ba ne amma zamani ne na zaman lafiya.
Shi ma Rabaran Muhammad Dan’Amarya y ace yankin Irigwe ya kasance gida ga Fulani mabiya addinin Kirista saboda cibiya da suka dashi a yankin na gudanar da taronsu na kasa da kasa. Yayi addu’ar Allah ya kawar da tashin hankali, wadanda kuma suke da mummunar niyya Allah ya basu damar tuba. Ya godewa al’ummar Irigwe da suak ce sun yafe.
General Isiyaku Dikko mai ritaya wanda ya shugabanci kungiyar Hausa, Fulani da Kanuri mabiya addinin Kirista ya yi kira jama’a da su rungumi zaman lafiya da juna domin a samu ci gaban rayuwa. Yace hakuri shi ne maganin zaman duniya saboda tilas ne a samu sabani da juna wani lokacin musamman ma tsakanin Fulani masu kiwo da manoma.
Sarkin Irigwe Ronku Aka y ace ya ji dadin ziyarasu saboda sun yi masu kalmomi masu kyau dake faranta zuciya.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani
Facebook Forum