Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a yunkurin da takeyi na ganin tasamu shiga jerin kungiyoyi hudu, daga saman teburin firimiya lig na kasar Ingila a bana yana fuskanatar kalu bale.
Arsenal ta samu koma bayan hakanne bayan da kungiyar kwallon kafa ta Everton ta doketa da kwallo daya mai ban haushi a ranar Lahadi da ta gabata cikin wasan mako na 33, a Goodison Park.
Dan wasan Everton, Phil Jagielka, ne ya jefa kwallon a ragar Arsenal tun a minti na 10 da fara wasan.
Rashin nasarar da Arsenal ta yi ya sa ba za ta koma ta uku a kan teburi ba, bayan karawar mako na 33, Tottenham ce ta ci gaba da zama a gurbin da maki 64, yayinda ita Arsenal take da maki 63.
Arsenal tana da maki dai dai da Chelsea wanda take matsayi na biyar da maki 63, banbancin kwallaye ya rabasu inda a ranar Litinin zata buga wasanta da Westham, da zaran ta samu nasara a wasan zata koma matsayi na hudu da maki 66, inda Arsenal zata dawo matsayi na biyar,
Wanda hakan na iya haramta mata halartar gasar cin kofin zakarun Turai UEFA Champion League na shekarar 2019/2020.
Arsenal dai zata buga wasanta na gaba da kungiyar Watford, ranar Litinin 15 ga watan Afirilun bana.
Facebook Forum