Ta hanyar bawa kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama umarnin kin daukar duk wani namiji dan Sudan ta Kudu da ya yi yunkurin shiga jirgi don barin kasar daga filin jirgin sama na Juba babban birnin kasar.
Dama masu shiga Uganda ta mota daga iyakar Nimule. Amnesty din na kira ga gwamnatin Sudan ta Kudu din data tabbatar jama’a za su iya shige da fice daga kasar zuwa wata kasa.
Sannan su tabbatar da masu gujewa tashin hankalin kasar na da damar ficewa bisa kariyar lafiyarsa da tabbaci.
Wakilin Sudan ta Kudu a majalisar dinkin duniya Akuei Bona Malual ya musanta zargin na cewa gwamnatinsu na hana ‘yan Sudan ta Kudu ficewa daga cikin kasar kamar yadda Amnesty suka bayyana.