Daga ranar sha biyar ga wannan watan duk mai sana'ar canjin kudin waje da bai ajiye nera miliyan talatin zuwa saba'in to ya kwana da sanin cewa babban bankin Najeriya zai karbi lasisinsa kana ya mayar masa da kudin ajiyarsa na dalar Amurka dubu ashirin da ya bayar kudin ajiyar farko.
Sabuwar dokar tace tsohon mai ragista zai biya nera miliyan talatin da biyar ne shi kuma sabon shiga ya biya nera miliyan saba'in. Wato miliyan talatin da biyar kudin ragista kana talatin da biyar kuma kudin kafin alkalamin jarinsa sabanin dala dubu ashirin da suke biya kwatankwacin nera miliyan uku.
Masu sana'ar sun gudanar da taronsu a birnin Iko game da lamarin da suka ce ya fi karfinsu. Wakilin Muryar Amurka ya kira babban darakta a babban bankin Najeriya domin ya ji abun da zasu yi su taimakawa masu sana'ar canjin. Daraktan yace sun gana da jami'an babban bankin kuma an lura da duka karafe-korafensu to sai dai mahukuntan bankin basu zauna sun dubasu tukunna ba.
Daraktan yace babban bankin ya dauki matakin ne da nufin tsarkake harkokin tattalin arzikin kasa. Shugaban 'yan canjin Alhaji Aminu Gwadabe yace cikin masu sana'ar kashi tamanin da biyar basu da irin kudin da ake bukata. Saidai idan manufar ana son a karbe sana'ar ce daga hannunsu ko kuma a jefa jama'a da dama cikin rashin aikin yi su ne zasu sa a nemi irin makudan kudaden.
Alhaji Gwadabe yace sana'ar canji ta bayar da ayyuka ga mutane. Ta taimaka wurin tsayar da farashin dala da sauran kudaden kasashen waje. Dan kasuwa ya san farashin dala sabili da sana'arsu. Sun taimaka sun kawar da kudin jabu.
Alhaji Shehu Anka yace a ce su ajiye miliyan talatin da biyar ba kuma riba za'a basu ba akwai wata manufa daban.
'Yan canjin sun ce ban da karin kudi da aka yi masu lokacin da aka diba yayi kadan ainun. Kamata yayi a yi masu yadda aka yiwa bankuna lokacin da aka ce su kara jarinsu. An basu shekara daya. Shin wai me yasa su ma ba za'a basu akalla shekara daya ba.
Ga rahoton Ldan Ibrahim Ayawa