A Gabon kotun tsarin mulkin kasar ta tabbatar da zaben shugaban kasar Ali Bongo, a zaman wanda ya lashe zaben shugabanci kasar da aka yi cikin watan jiya, wanda ya fadada mulkin zuriyarsa zuwa shekaru 40 a kasar mai arzikin mai da Afirka ta tsakiya.
Kotun tayi watsi da kalubalen da babban abokin takarar Bongo Jean Ping yayi na neman a sake kidaya kuri'un bisa zargin an tafka magudi.
Bayan da aka bada sanarwar sakamakon zaben, shugaba Ali Bongo, yayi kira da a gudanar tattaunawa tsakanin al'umar kasar.
Amma bayanda kotun ta bada sanarwar, anji wani kakakin Mr. Ping yana gayawa kamfanin dillancin labarai na kasar Faransa cewa, Mr. Ping ne ya lashe zaben kasar.